RMC Hausa
LIVE Radio

GWAMNAN KATSINA SABON NAƊI

Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya amince da nadin sabbin Sakatarorin Dindindin guda uku a Ma’aikatan Jihar Katsina.

Sanarwar hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Shugaban Ma’aikatan Jihar, Mallam Falalu Bawale, ya fitar.

Sabbin Sakatarorin Dindindin da aka nada su ne: Tukur Hassan Dan Ali daga Karamar Hukumar Danmusa — fitaccen ɗan jarida kuma Shugaban Majalisar Ƙungiyar ‘Yan Jarida ta Najeriya (NUJ) reshen Jihar Katsina; 

Junaidu Muntari daga Karamar Hukumar Kankara; da Yahaya Abdullahi daga Karamar Hukumar Safana.

Da yake tsokaci kan nadin, Shugaban Ma’aikatan Jihar, Mallam Falalu Bawale, ya bayyana cewa nadin ya ta’allaka ne bisa cancanta kawai.

Ya ce sabbin Sakatarorin Dindindin sun samu nasarar tsallakewa tare da cin jarabawar da aka shirya bisa tsarin cancanta, wadda Cibiyar Horas da Ma’aikatan Gwamnati ta Najeriya (Public Service Institute of Nigeria) ta gudanar a madadin Gwamnatin Jihar Katsina.

Bawale ya ƙara da cewa tsarin zaɓen na nuna jajircewar gwamnatin wajen ɗora al’amuran ma’aikata kan ƙwarewa da kwarewar aiki, yana mai jaddada cewa sauye-sauyen da ake aiwatarwa a ma’aikatan gwamnati sun ta’allaka ne kan cancanta, ingantaccen aiki da gaskiya.

Haka kuma, an ƙarfafa sabbin waɗanda aka nada su rungumi cikakken tsare-tsaren gwamnatin na “Building Your Future”, duba da muhimmancin matsayinsu wajen haɓaka tattalin arziki da ci gaban zamantakewar al’ummar Jihar Katsina.

Bawale ya ja hankalin Sakatarorin Dindindin da su cika tsammanin jama’a, inda ya ce: “Dole ne ku tabbatar da amincewar da aka ɗora muku ta hanyar aiwatar da ayyukanku da jajircewa, ƙwarewa da cikakken sadaukarwa domin bunƙasa da daidaita aikin ma’aikatan Jihar Katsina.”

Nadin ya fara aiki nan take, yayin da gwamnatin ke ƙara ƙaimi wajen sake fasalin ma’aikatan gwamnati domin samar da ingantacciyar hidima ga al’umma a faɗin jihar.

Ibrahim Kaula Mohammed
Babban Sakataren Yaɗa Labarai ga Gwamna, Jihar Katsina
6 ga Janairu, 2026

RMC HAUSA 

Post a Comment

Previous Post Next Post