RMC Hausa
LIVE Radio

KASUWAR CHARANCI

Gwamnatin ƙaramar hukumar Charanci ta umurci 'yan kasuwa masu saye da sayarwa a bakin kasuwar garin Charanci bisa hanyar Katsina zuwa Kano dasu tashi, domin rage cunkoso da kiyaye haɗurra da gobara a kasuwar. 

Shugaban ƙaramar hukumar Charanci Hon. Ibrahim Sani Koda ya bayyana bada wannan umurnin a ranar laraba 7/01/2026, a ofishinsa yayin da ya kira wani taron masu ruwa da tsaki akan lamarin. 

Kiran taron da shugaban ƙaramar hukumar ya yi, ya biyo bayan samun cunkoso da haɗurra da gobara da ake samu a kasuwar, wanda ko a satin da ya gabata an samu haɗarin gobara a kasuwar garin ta Charanci, wanda ya yi sanadiyar asarar dukiya ta miliyoyin nairori. 

Sannan shugaban ƙaramar hukumar ya kuma bayyana tada tashar garin Charanci zuwa kasuwar zamani ta garin Charanci wadda aka gina lokacin mulkin tsohon Gwamna Shema. 

Shugaban ƙaramar hukumar ya bayyana wasu tsare, tsare masu ma'ana da za a aiwatar dasu, a tsohuwar tashar motar ta Charanci domin bunƙasa samar da kuɗaɗen shigar ƙaramar hukumar, sannan kuma hakan zai sauƙaƙa masu aikin tagwayen hanyoyi daga Katsina zuwa Kano da suke gab da shigowa garin Charanci. 

Sannan ya ƙara da cewa" anyi tanadi na musamman ga mutanen da abun ya shafa domin rage masu raɗaɗi, duba yanayin da zasu samu kansu sanadiyar tada su daga wuraren sana'ar su. 

Da yake gabatar da jawabi a wurin taron, Sarkin Shanun Katsina Hakimin Charanci Alhaji Abashe Abdulkadir ya nuna jin daɗin shi akan wannan yunkuri, kuma su na masu bada cikakken goyon bayansu akan wannan ci gaba, za ayi shela a sanar da mutane. 

Sarkin Shanun Katsina Alh. Abashe Abdulkadir ya ci gaba da gargaɗi tare da faɗi da babbar murya ga duk wanda aka samu ya yi kunnen kashi akan wannan umurni, to zai fuskanci hushin hukuma domin ba zasuyi sakaci da wannan ci gaba da aka samu ba. 

Mutane da dama ne su ka tofa albarkacin bakinsu, a wurin taron, sun kuma yaba ma Shugaban ƙaramar hukumar tare da goyon bayan wannan kudiri.

Sannan sun kara da bada wasu shawarwari masu mahimmanci da zasu ƙara ciyar da ƙaramar hukumar gaba a wannan fuska da sauran wasu batutuwa da su ka shafi ci gaban ƙaramar hukumar.

Daga cikin masu ruwa da tsaki da su ka halarci taron, akwai mataimakin shugaban Jam'iyyar Apc mai kula da shiyyar Katsina Alhaji Yahaya Idris Asasanta, shugaban Jam'iyyar Apc na ƙaramar hukumar Charanci, shugabannin tsaro na ƙaramar hukumar. Da dai sauran su.

RMC HAUSA 

Post a Comment

Previous Post Next Post