Manchester United ta sallami kocinta ɗan asalin Portugal, Ruben Amorim bayan ya soki shugabannin ƙungiyar a ƙarshen makon jiya.
Ana kallon korar tasa a matsayin wani tsattsauran hukunci daga shugabannin ƙungiyar, waɗanda ya soka a ƙarshen makon jiya.
Amorim mai shekaru 40, ya bar United ne watanni 14 bayan kama aiki, inda ya gaza farfaɗo da tagomashinta a kaka biyu da ya jagoranta.
Shin ko ya magoya bayan ƙungiyar ƙwallon ƙafar ke kallon wannan lamari?
RMC HAUSA