RMC Hausa
LIVE Radio

ABBA NE MAGAJIN MALAM

"Abba Kabir ne magajin Malam Aminu Kano wajen kishin jahar Kano." 

Kalaman Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ke nan kan gwamnan Jihar Kano Abba Kabiru Yusuf a cikin wani sakon taya gwamnan murnar cikarsa shekaru 63, wanda kakakin Tinubun Bayo Onanuga ya fitar.

Tinubu ya ce sauƙin kai, ƙasƙantar da kai da kuma jajircewar gwamnan sun bayyana ƙarara a yadda yake tafiyar da al'muran Jihar Kano.

Ya ci gaba da cewa "Ina da tabbacin ka biyo hangen nesa irin na Malam Aminu Kano a siyasar ci-gaba, da bunƙasa ci-gaba tun daga tushe da kuma ceton talakawa."

Tinubu ya kuma yaba wa Gwamna Abba wajen ayyukan ƙawata birnin da suka hada sabunta birane da gina tituna da gadoji. 

Sannan ya jinjina masa wajen ayyana dokar ta-ɓaci a ɓangaren ilimi, abin da a cewarsa ya sa Kano ta samu gagarumar nasara a jarrabawar NECO.

RMC HAUSA 

Post a Comment

Previous Post Next Post