Gwamna Abba Gida Gida ya yi sabbin nade-naden mukamai cikin wata sanarwa da kakakin gwamnan jihar, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Laraba.
A cewar sanarwar, Hon. Abdulkadir Balarabe Kankarofi (Alhajiji) an nada shi a matsayin mai ba gwamna shawara na musamman kan harkokin jin-kai.
Haka kuma, an nada Hajia Aisha Tamburawa a matsayin mai ba Gwamna Shawara ta Musamman kan yaɗa Kyakkyawan manufofi. Sai Engr. Mukhtar Yusuf a matsayin Manajan Darakta na Hukumar WRECA, Yayin da Zakari Usman Bala ya kasance matsayin Mataimakin Manajan Darakta na WRECA
Sannan kuma an nada Dr. Mukhtar Bello Maisudan, a matsayin Sakataren Zartarwa na Hukumar Tallafin Karatu ta Jihar Engr. Ya yayin da Abba Kankarofi ya samu matsayin Darakta na Hukumar Kula da Gyaran Hanyoyi ta Jihar Kano (KARMA).
Har'ila yau an nada Hon. Musayyib Kawu Ungoggo a matsayin Manajan Darakta na gidan Zoo.
Gwamna Yusuf ya bukaci sabbin wadanda aka nada da su tabbatar da amincewar da aka dora musu ta hanyar nuna jajircewa, gaskiya da kuma sadaukarwa ga al’ummar Jihar Kano.
RMC HAUSA
Category
Siyasa