Sako zuwa ga Gwamnan Jihar Katsina Malam Dikko Radda daga Al'ummar Kauyen Unguwar Mantau dake Karamar Hukumar Malunfashi.
Al'ummar Kauyen Unguwar Mantau dake a Karamar Hukumar Malunfashi Sunyi Godia a Gwamnan Jahar Katsina Malam Dikko Umar Radda da ya cika masu Alkawarul daya dauka na gina masu masallaci da Makaranta da Hanya da Bayyar da tallafi ga marayu
Al'ummar sunyi Godiyar ne a lokachin da suke zantawa da Manema labarai a cikin kauyen Unguwar Mantau
Haka zalika Al'ummar Sun bayyana cewa cikin alqawari guda 5 da gwamnan yayi masu an fara bada tallafi ga marayu da Kuma fara Aikin Gina Asibiti da aikin Gina makaranta
Sauran Kuma Suna da Tabbacin tunda yayi alqawarin Sunsan zai cika
Al'ummar Sunyi kira ga gwaman da ya maida Hankali wajen Gina masu hanyar duba da tun kafin su shiga matsa Tsaro Ciwonsu guda dayane na Rashi wannan Hanyar.
Sunyi nuni da cewa ko shakka babu idan aka gama wannan hanyar zata taimaka Gaya wajen Rage masu tsadar kayayyaki da Kuma bunkasa tattalin arzikin yankin
Al'ummar da sukai Kiran sun hada da Jagoran dake kula da aikin Malam Zuladaini Ibrahim da Rayyanu Adamu Mantau da Nasiru Adamu dadai sauransu.
RMC HAUSA
Category
Labarai