BARAU MALIYA
Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Barau I. Jibril ya bayyana cikakken matsayinsa a siyasa, inda ya umarci dukkan magoya bayansa da su marawa Gwamnan Jihar Kano, Engr. Abba Kabir Yusuf (Abba Gida-Gida) baya, bayan karɓarsa zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC).
Sanatan ya yi wannan jawabi ne a yayin taron karɓar Gwamna Abba Kabir Yusuf zuwa APC, bayan da gwamnan ya fice daga jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP), lamarin da ya ɗauki hankalin jama’a da masu ruwa da tsaki a fagen siyasar Kano.
RMC HAUSA
Category
Siyasa