Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umar Raɗɗa yayi addu’a tare da fatan alkairi ga tawagar wakilan matan jihar Katsina akan hanyar su ta zuwa jihar Kaduna domin halartar wani muhimman taro.
Tawagar wakilan matan jihar Katsina sun tafi jihar Kaduna domin halartar taron bayar da dama ga mata wajen shiga harkokin siyasa wato Reserved Seat for Women Bill, wanda ofishin shugabar matan jam’iyyar APC ta ƙasa ke jagoranta.
Taron wanda ya shafi jihohin Arewa maso Yamma (North West) na da nufin ƙarfafa gwiwar mata da kuma wayar da kan su kan muhimmancin samun wakilci na musamman a majalisun dokoki da sauran muhimman matakan shugabanci a ƙasar nan.
A gabanin tafiya, tawagar ta hadu da mai girma Gwamnan jihar Katsina Katsina Malam Dikko Umaru Radda inda yayi masu addu’a da fatan alheri.
Tawagar matan, Katsina ƙarƙashin jagorancin shugabar kungiyar matan Hajiya Zainab Abdulhadi Tafashiya, ta baro jihar Katsina zuwa jihar Kaduna domin halartar wannan muhimmin taro a yau Laraba 28/1/2026.
Ana sa ran taron zai samar da shawarwari da dabaru da za su taimaka wajen tabbatar da amincewa da kudirin dokar Reserved Seat for Women Bill, tare da ƙarfafa haɗin kai tsakanin matan jam’iyyar APC a shiyyar Arewa maso Yamma.
Category
Siyasa