Farfesa Umar Sani Fagge ne ya bayyana hakan yayin gabatar da muƙala kan yadda masu tafsiri a lokacin azumi za su ja hankalin al’umma kan matsalar tsaro da ake fama da ita a halin yanzu.
Ya ƙara da cewa duk wanda ke son fassara Alƙur’ani mai girma dole ne ya tanadi ilimi da kayan aikin da suka dace kafin ya zama mai gabatar da tafsiri, domin kauce wa sanya ruɗani a cikin al’umma.
Shi ma Farfesa Ahmad Murtala, Shugaban Sashen Nazarin Alƙur’ani na Jami’ar Bayero, ya ce an shirya taron ne domin faɗakar da malamai masu tafsiri a watan Ramadan kan yadda za su ja hankalin al’umma wajen inganta tsaro, zaman lafiya da sauran muhimman batutuwa.
A nasa jawabin, bako na musamman kuma Babban Limamin Kano, Farfesa Sani Zahraddeen, wanda Farfesa Nu’uman ya wakilta, ya yi kira ga mahalarta taron da su yi amfani da abin da suka koya wajen isar da saƙo mai amfani ga al’umma.
Makasudin taron, wanda Jami’ar Bayero ta shirya ƙarƙashin Sashin Nazarin Alƙur’ani da Iliminsa, shi ne wayar da kan malamai masu tafsiri a watan Ramadan kan muhimmancin tafsiri bisa ƙa’ida da kuma yadda za su taimaka wajen gina al’umma.
Category
labarai