Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya sha alwashin cewa Nigeria za ta yi nasara a kan matsalar ta'addanci da ta ɓarayin daji, yana mai bayyana barazanar tsaron da ƙasar ke fusanta a matsayin wani abu da "ba za a amince da shi ba".
Shugaban ya bayyana haka ne yayin buɗe Taron Majalisar Tattalin Arziki ta Ƙasa karo na biyu a fadar gwamnatin Nijeriya da ke Abuja a ranar Litinin.
Tibubu ya tabbatar wa 'yan Nijeriya ƙudirin da gwamnatinsa ta ɗauka na ƙarfafa dakarun tsaron ƙasar da mai do da zaman lafiya a wuraren da ake fama da matsalar tsaro.
RMC HAUSA
Category
Labarai