RMC Hausa
LIVE Radio

SABUWAR MAKARANTA

Amb. Isah Dodo Ibrahim Unguwar Alkali ya sadaukar da gidan da ya gada daga iyaye da kakanni kyauta wato (Waqaf) inda aka mayar da shi Islamiyya da wurin koyar da abubuwan da suka shafi addinin musulunci.

A ranar laraba 11-02-2026 Mai Martaba Sarkin Katsina Dr Abdulmuminu Kabir Usman ya jagoranci bude ginin Islamiyyar dake a Unguwar Alkali nan cikin garin Katsina. 

Da yake gabatar da jawabin sa Amb. Isah Dodo Ibrahim yayi godiya ga Allah SWT da ya nuna masa wannan rana wadda akazo domin shaida wannan aiki, wanda ya dade yanaso ya aiwatar. 

Ya bayyana wannan gini mai dadden tarihi wanda ya gada daga iyaye da kakanni kuma yaga babu abinda ya dace sai ya mayar da shi wurin da za'a rika koyar da Alkur'ani da sauran littafai.

Da yake gabatar da jawabin mai kula da makarantar Dr. Idris Balarabe ya bayyana irin shirin da akayi ma makarantar musamman samar da malamai masu nagarta, kwamfutoci, hasken lantarki mai amfani da hasken rana da dai sauran su. Kuna akwai bangaren Islamiyya da hadda a wurin.

Da yake gabatar da jawabin sa albarka mai martaba Sarkin Katsina Dr Abdulmuminu Kabir Usman ya yabama Amb. Isah Dodo Ibrahim bisa wannan kokari da abun alkairi da yayi, tabbas wannan shine abunda ake bukata a cikin al'umma. 

A samu wanda zai gina inda al'umma zasu rika samun ilimin bauta ma Allah, domin sai mutum nada ilimi ne zai iya bautar Allah, daga karshe yayi kira ga al'umma dasu yi koyi da shi tare da rokon Allah ya saka masa da aljanna. 

Mutane da dama ne suka gabatar da jawabai a wurin taron musanman na godiya ga Amb Abubakar Dodo wanda suka hada da Alh. Maude Yusuf da dai sauran su.

Post a Comment

Previous Post Next Post