TAKAITACCEN RAHOTO NA MANYAN NASARORIN SANATA ABDUL’AZIZ MUSA YAR’ADUA
Sanata Abdul’aziz Musa Yar’adua ya aiwatar da ayyuka masu yawa da suka shafi ci gaban al’umma a mazabar Katsina ta Tsakiya, waɗanda suka haɗa da:
1. Ƙarfafa Matasa da Mata
• Raba babura 125 da injinan ɗinki 218.
• Horas da matasa da mata kan sana’o’i tare da tallafin jari.
• Tallafawa masu nakasa da kayan aiki da kuɗi.
• Ƙarfafa ‘yan kasuwa 400 da POS, takardun CAC da kuɗi.
2. Harkar Wutar Lantarki (Solar)
• Horas da matasa kan girka da gyaran solar.
• Ba su kayan aiki, janareta na gida da kuɗi bayan horo.
3. Wayar da Kai
• Shirya tarurruka kan yaƙi da shaye-shaye da rikicin matasa, tare da ba mahalarta kuɗi da takardu.
4. Tallafin Agaji
• Raba kayan abinci da kuɗi ga waɗanda ambaliya da wasu bala’o’i suka shafa.
• Raba tallafin Ramadan na daruruwan miliyoyin naira a shekarun 2024–2026.
• Taimakawa marasa galihu da waɗanda suka rasa ‘yan uwa.
5. ICT da Fasahar Zamani
• Horas da ɗalibai 250 kan kwamfuta.
• Ba matasa 75 horo kan digital skills da AI tare da laptop.
6. Shirye-shiryen Tallafin Gwamnati
• Taimaka wajen samar da shirin CCT, MarketMoni da sauran tallafi ga dubban jama’a.
7. Noma
• Raba takin zamani dubban buhu.
• Ba manoma kayan aikin noma.
• Horas da matasa kan noman dabino da shea.
8. Lafiya
• Samar da kayan ajiyar gawa na zamani a asibiti.
• Gina da gyara cibiyoyin lafiya.
• Shirya aikin tiyata da bayar da magunguna kyauta.
• Biyan kuɗin jinya ga marasa lafiya.
9. Ilimi
• Raba littattafai da kayan koyarwa.
• Biyan kuɗin rajistar ɗalibai.
• Tallafawa makarantu, malamai da ɗalibai masu nakasa.
• Gyara makarantu da cibiyoyin addini.
10. Tsaro
• Ba jami’an tsaro babura da motoci.
• Samar da hasken titi na solar.
• Tallafawa ‘yan banga da waɗanda rikici ya shafa.
11. Tallafin Iyali
• Ba marayu mata kayan ɗaki.
• Taimakawa bukukuwan aure da suna.
12. Ci gaban Al’umma
• Samar da rijiyoyin burtsatse (boreholes) da wutar lantarki.
• Gyaran hanyoyi da sauran ayyukan raya ƙasa.
• Tallafawa gidajen marayu da fursunoni masu bashi.
13. Samar da Ayyukan Yi
• Samawa matasa aiki a rundunonin tsaro da hukumomin gwamnati.
14. Siyasa da Jagoranci
• Tallafawa jam’iyya da ‘yan takara.
• Gabatar da kudurori da dokoki a majalisar dattawa.
15. Manyan Nasarori
• Shugaban Northern Senators Forum.
• Shugaban Kwamitin Sojojin Kasa a Majalisar Dattawa.
• Kafa kwamiti na kula da bukatun mazaba domin tabbatar da gaskiya da ingantaccen aiki.
Sen. Abdu Soja Media Team