RMC Hausa
LIVE Radio

SANATA SOJA YA RABA KAYAN AZUMI

Sanata Abdul’aziz Musa Yar’adua Ya Kaddamar da Rabon Kayan Abincin Ramadan na 2026 ga Al’ummar Mazabar Katsina ta Tsakiya

Sanatan da ke wakiltar mazabar Katsina ta Tsakiya a Majalisar Dattawa, Abdul’aziz Musa Yar’adua, ya kaddamar da rabon kayan abinci na watan Ramadan na shekarar 2026 ga al’ummar mazabarsa, kamar yadda ya saba yi a kowace shekara domin tallafa wa jama’a a wannan wata mai alfarma.

Shirin rabon kayan abincin wanda ya zama daya daga cikin manyan tsare-tsaren jin kai na Sanatan, ana sa ran kimanin mutane dubu goma sha takwas (18,000) ne za su amfana daga tallafin, wanda ya kunshi rukunoni daban-daban na al’umma domin tabbatar da cewa tallafin ya kai ga masu bukata a fadin mazabar.

A rukuni na farko, wadanda za su amfana sun hada da shugabannin jam’iyya tun daga matakin jiha, kananan hukumomi da mazabu, har da delegates, shugabannin kananan hukumomi da mataimakansu, hakimai da magaddai, malaman addini, kansiloli, da kuma ‘yan kwamitin Sanatan a kowace karamar hukuma, tare da sauran magoya bayansa a matakin mazabu.

Hakazalika, a rukuni na biyu, an tanadi tallafin ne domin kungiyoyin addini da na siyasa, matasa, ‘yan jarida, kungiyoyi masu zaman kansu, dattawa, masu ruwa da tsaki a al’umma da kuma dimbin magoya bayan Sanatan. Haka kuma makwabta, ‘yan’uwa da abokan arziki da yan midiya na shi suma ba a barsu a baya ba, domin suma suna cikin wadanda za su ci gajiyar wannan tallafi.

Bugu da kari, daraktocin yakin neman zaben Sanatan da mataimakansu, tare da kwamitin zartarwar sa na mazabar Katsina ta Tsakiya da sauran manyan masu ruwa da tsaki, duk suna cikin jerin wadanda aka tanadar musu da wannan tallafi.

Wannan shiri na rabon kayan abincin Ramadan na daga cikin matakan da Sanata Abdul’aziz Musa Yar’adua ke dauka domin saukaka wa al’umma halin da suke ciki, musamman a wannan lokaci na ibada, tare da karfafa dankon zumunci da hadin kai a tsakanin al’ummar mazabar Katsina ta Tsakiya.

Al’umma da dama sun bayyana jin dadinsu da godiya ga Sanatan bisa wannan gagarumin tallafi, inda suka bayyana cewa irin wadannan ayyuka na jin kai na kara tabbatar da kusancin sa da jama’a da kuma jajircewarsa wajen inganta rayuwar al’ummar da yake wakilta.

Sen. Abdu Soja Media Team.

Post a Comment

Previous Post Next Post