Ƙasar Iran Ta Gindaya Sharadi Kan Wucewa Ta Mashigar Strait of Hormuz.
Rahotanni daga Iran sun bayyana cewa dakarun juyin juya halin ƙasar sun sanar da cewa za su buɗe mashigar ruwan Strait of Hormuz ga wasu ƙasashen duniya domin jigilar man fetur da iskar gas.
Sai dai sun gindaya sharadi guda kafin hakan ta tabbata.
A cewar sanarwar, duk wata ƙasa — ta Larabawa ko ta Turai — da ta kori jakadan Isra’ila da na Amurika daga ƙasarta, za a ba ta cikakken izini ta rika wucewa ta mashigar ruwan Strait of Hormuz domin gudanar da harkokin makamashi.
Sanarwar ta ce wannan mataki zai fara aiki daga ranar Talata, yayin da aka buƙaci ƙasashen da ke son amfani da mashigar su dauki wannan mataki domin samun damar wucewa cikin sauƙi.
Masu lura da al’amuran siyasar duniya na ganin cewa idan wannan mataki ya tabbata, zai iya ƙara sauya yanayin rikicin da ke faruwa a Gabas ta Tsakiya, musamman a bangaren kasuwancin man fetur a duniya.
Category
Labarai