RMC Hausa
LIVE Radio

ƘWACEN WAYA

Matasa biyu sun rasu yayin tserewa masu kwacen waya a Kano
 
Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta tabbatar da mutuwar wasu samari biyu da suka fada wani kududdufi a yankin Ring Road Kureken Sani, Kumbotso, yayin da suke kokarin tserewa daga masu kwacen waya. Jaridar Daily Trust ta ruwaito hukumar na cewa Sadiq Isyaku da Auwal Isyaku sun fada cikin kududdufin ne a daren ranar Juma’ar da ta gabata, inda aka ciro su ba sa cikin hayyacinsu, daga bisani kuma aka tabbatar da rasuwarsu.

Post a Comment

Previous Post Next Post