Ƙungiyar Uwar matasa Foundation haɗin gwiwa da Remi Tinibu support organization da Zulaihat Dikko Raɗɗa Foundation sun kai ziyarar girmamawa da kuma neman shawara ga Co-odinetan renewed hope na jihar katsina Alh.Tukur Jiƙamshi a gidansa da ke kofar kaura Layout katsina a ranar Litinin bisa jagorancin shugabar tafiyar Hajiya Zilaia Adamu Uwar matasa.
Inda aka tattauna batutuwa masu muhimmanci dangane da tafiyar da kuma samun goyon baya daga Alh.Tukur Jiƙamshi a kan tafiyar ta siyasa.
Category
Siyasa