Shugaba Donald Trump ya sake jaddada ikirarinsa na cewa Amurka da Iran za su hada gwiwa wajen kwashe sinadarin Uranium daga cibiyoyin nukiliyar kasar ta hanyar amfani da manyan katafilolin tone kasa (Excavators) a karkashin kowace irin yarjejeniyar zaman lafiya, kafin a kwashe kayayyakin zuwa yankin Amurka.
Kalaman na Trump na ranar Jumma’a sun zo ne duk da cewa Ma’aikatar Harkokin wajen Iran ta bayyana a baya cewa ajiyayyen sinadarin Uranium da Iran take da shi ba za a taba kai shi “ko ina ba."
Ko ya ku ke ganin wannan sabon tashintashina da Trump ke ƙoƙarin tadowa.