*SABUWAR DOKA*
Gwamnatin Jihar Katsina ta fitar da sabbin matakan tsaro domin daƙile ayyukan ’yanbindiga da masu garkuwa da mutane a jihar.
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar, Ibrahim Kaula Mohammed, ya fitar, gwamnatin ta haramta saye, sayarwa, jigilar manfetur da adana shi a cikin jarkoki a faɗin jihar baki ɗaya.
Haka kuma, an rufe dukkan harkokin POS da wuraren cajin waya na kasuwanci a ƙananan hukumomin Matazu da Musawa. Bugu da ƙari, a cewar sanarwar, an haramta amfani da babura a yankunan biyu saboda rahotannin tsaro da suka nuna cewa masu aikata laifuka na amfani da su wajen gudanar da ayyukansu.
A cewar gwamnatin, ta ɗauki matakan ne bayan taron gaggawa kan tsaro da Gwamnan jihar, Malam Dikko Umaru Radda ya jagoranta tare da jami’an tsaro, sarakunan gargajiya da sauran masu ruwa da tsaki.
Gwamnatin ta ce bincike ya nuna cewa masu laifi na amfani da man fetur, cibiyoyin POS da wuraren cajin waya wajen sauƙaƙa ayyukansu, don haka aka ɗauki matakan domin katse hanyoyin da suke amfani da su.
Sanarwar ta bayyana cewa sabbin dokokin sun fara aiki nan take, tare da gargaɗin cewa za a hukunta duk wanda aka samu ya karya umarnin.