RMC Hausa
LIVE Radio

NAƊIN SARAUTA A KANO

Obasanjo Kwankwaso da Tambuwal sun halarci bikin naɗa Abubakar Mahmoud a matsayin Garkuwan Kano a fadar sarkin kano.
Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo da gwamnan Jihar Kano kuma ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam'iyyar NDC, da tsohon gwamnan jihar kano Sen Rabi'u Musa Kwankwaso da tsohon gwamnan jihar Sokoto Rt Hon Aminu Waziri Tambuwal sun halarci bikin naɗa Abubakar Balarabe Mahmoud da sarautar Garkuwan Kano a matsayin babban baƙo na musamman.

An gudanar da bikin cikin armashi a Fadar Sarkin Kano, inda Muhammadu Sanusi II ya naɗa Abubakar Mahmoud da wannan babbar sarauta ta gargajiya.

Bikin ya samu halartar fitattun mutane da manyan baƙi daga sassa daban-daban na ƙasar nan, waɗanda suka taru domin shaida wannan gagarumin biki.

 Hoto saif Hassan

Post a Comment

Previous Post Next Post