Ahmed Musa ya yi ritaya daga bugawa Najeriya ƙwallo bayan share shekara 15 yana wakiltar ƙasar.
Musa ya bugawa Najeriya wasanni sau 111, ya kuma taɓa lashe gasar cin kofin Afirka tare da jagorantar ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta ƙasar Super Eagles
A wani saƙo da ɗan wasan ya wallafa a shafinsa na X ya sanar da yin ritayar, inda ya zayyano tarin nasarorin da ya samu a tarihin shi na wakiltar ƙasar, yana mai bayyana hakan a matsayin wani abu da ba zai taɓa mantawa da shi ba.
RMC HAUSA