Tinubu Ya Gabatar da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 58.47 na Shekarar 2026.
Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya gabatar da daftarin kasafin kuɗin Tarayyar Nijeriya na shekarar 2026, wanda ya kai jimillar Naira tiriliyan ₦58.47, da nufin ƙarfafa tattalin arzikin ƙasa, inganta tsaro, bunƙasa ayyukan more rayuwa da kuma walwalar al’umma gaba ɗaya.
A cewar bayanan kasafin, gwamnati ta ware kuɗaɗe masu yawa ga muhimman sassa domin cimma burin bunƙasa ƙasa da kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
A bangaren tsaro da kare ƙasa, an ware Naira tiriliyan ₦5.41, domin ƙarfafa rundunonin tsaro, yaƙi da ta’addanci, da tabbatar da zaman lafiya a faɗin ƙasar.
Bangaren ayyukan more rayuwa ya samu Naira tiriliyan ₦3.56, inda aka tanadi kuɗaɗe domin gina hanyoyi, layukan dogo, wutar lantarki da sauran muhimman ababen more rayuwa.
Hakazalika, bangaren ilimi ya samu Naira tiriliyan ₦3.52, domin bunƙasa ilimi, inganta makarantu, da tallafa wa malamai da ɗalibai a matakai daban-daban.
Bangaren lafiya kuwa ya samu Naira tiriliyan ₦2.48, a ƙoƙarin gwamnati na inganta asibitoci, samar da kayan aiki na zamani, da ƙarfafa kiwon lafiyar al’umma.
Kasafin kuɗin na shekarar 2026 ya kasu gida biyu: Kuɗaɗen Ayyukan Ci Gaba (Capital Expenditure), wanda aka ware Naira tiriliyan 26.08, domin aiwatar da manyan ayyukan ci gaba da gina ƙasa.
Kuɗaɗen Gudanarwa ba tare da bashin kudi ba (Recurrent Expenditure), wanda aka tanadar masa Naira tiriliyan 15.25, domin biyan albashi, gudanar da ma’aikatun gwamnati da ayyukan yau da kullum.
Gwamnatin dai, ta gina kasafin ne bisa wasu muhimman hasashen tattalin arziki, ciki har da: Farashin gangar danyen mai; Dala $64.85 a kowace ganga, Yawan fitar da mai a rana; Gangar mai miliyan 1.84, Farashin musayar kuɗi; ₦1,400 kan kowace Dala ɗaya ta Amurka
Gwamnati ta bayyana cewar kasafin kuɗin na shekarar 2026 zai taimaka wajen bunƙasa tattalin arziki, samar da ayyukan yi, da kuma inganta rayuwar ‘yanNijeriya baki ɗaya.
RMC HAUSA
Category
labarai