RMC Hausa
LIVE Radio

USMANIYA RIMI CHARANCI ƁATAGARAWA

Dan majalisar tarayya mai wakiltar Kananan hukumomin Batagarawa, Charanchi da Rimi ya kaddamar da bada tallafin kudin karatu na fiye da Naira Milyan 80,000,000 ga Dalibai 3,500 a karo na ukku. 

A ranar Litinin 29/12/2025, Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Radda PhD CON wanda ya samu wakilcin mataimaki shi Hon. Faruk Lawal ya kaddamar da bada tallafi karatun.

Wanda Ɗan majalissar tarayya mai wakiltar Kananan hukumomin Batagarawa, Charanchi da Rimi Hon. Usman Murtala Banye ya samar na fiye da Naira Milyan 80 zuwa 100 ga ɗaliban 3,500 na Makarantun gaba da sakandire da suka fito daga ƙananan hukumomin ukku.

Tallafin da aka kasa shi gida ukku zuwa hudu inda kowanne zasu amfana da kaso kamar haka Masu karutun Digirin Digirgir zasu amfana da Naira Dubu Dari, Masu karatun Digiri na biyu zasu amfana da Naira Dubu Hamsin.

Ka zalika Masu karatun Digiri da Difloma ta biyu zasu amfana da Naira Dubu Ashirin da biyar, sai masu karatun Difloma da NCE da sauran kwasa kwasai zasu amfana da Naira dubu Ashirin da biyar. 

Da yake gabatar da jawabin shi Malam Dikko Radda ta bakin Hon. Faruk Lawal Joɓe Sarkin Fulani ya yaba da kokarin Hon. Usman Murtala Banye akan yadda yake jagoranci Mai inganci ga al'ummar da yake wakilta. 

Gwamnan yaci gaba da cewa Hon.Usman Banye kowace al'umma tana bukatar mutum irin shi domin yana ayyukan alkhairi lungu da sako na inda yake wakilta.

Daga karshe wakilin gwamnan ya bayyana nasarorin da gwamnatin jihar ta samu ta bangaren ilimi tun hawan su, ya kuma yi godiya a madadin gwamnatin jihar Katsina akan abinda Hon. Usman Murtala Banye ya ya yi.

Shima a nashi jawabin Hon. Usman Murtala Banye ya bayyana cewa abinda zasu aiwatar a yau, sun samo shi ne daga Gwamnati tarayya da wannan ne suke godiya ga shugaban kasa Sanata Bola Ahmad Tinubu akan wannan ƙoƙari da yake yi masu.

Hon. Banye ya kuma godema Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Radda PhD CON wanda shima tsaye yake wajen bada sharawa domin ganin al'umma sunci gaba.

Ka zalika ya yi godiya ga dukkan masu ruwa da tsaki tare da dalibai da zasu amfana da tallafin akan goyan bayan da suke basu, ya kuma roki wakilin gwamna da ya kara yi ma shi godiya ga dukkan masu ruwa da tsaki akan goyan baya da suke ba shi.

Da karshe ya bukaci wanda suka amfana da tallafin dasu tafiya dashi ta hanyar da ya dace wajen gudanar da karatun su domin cigaban su.

Mutane da dama suka tofa albarkaci bakin su daga ciki akwai shugaban rukunin kamfanin Continental Alh. Salisu Mamman kadandani, Kauran Katsina Alh. Aminu Nuhu Abdulkadir da sauran su.

Taron wanda ya gudana a Babban dakin taro na Continental Event Centre ya samu halartar shugabannin kananan hukumomin Batagarawa, Charanchi da Rimi tare da masu ruwa da tsaki na kananan hukumomin.

Sarkin kurayen Katsina Hakimin kuraye Alh. Usman Darda'u Kuraye, Tsohon Dan Majalissar Tarayya Hon. Lema u Tsagero Dalibai da sauran Al'umma.

RMC HAUSA 

Post a Comment

Previous Post Next Post