RMC Hausa
LIVE Radio

AIKIN ALKAIRI

Gidauniyar "Grassroot Charitable Humanity Foundation" ta biya ma mutum 30 maza da mata bashi dake ɗaure a gidan gyaran hali a Katsina. 

A ranar Alhamis Gidauniyar ƙarƙashin jagorancin Hajiya Nasiba Umar Kofar Bai tare da tawagarta, ta ziyarci gidan gyaran hali dake Katsina ta biyama mutum 30 maza da mata bashi wanda ya yi sanadiyar ɗaure su, a gidan gyaran hali. 

Wannan aiki da Gidauniyar tayi yana cikin aikace-aikacen da Gidauniyar takeyi domin taimakon Al'umma, bayan wannan Gidauniyar tana taimakon marayu, marasa ƙarfi, gajiyayyu. Da dai sauran ayyukan taimakon Al'umma maza da mata. 

Tawagar Gidauniyar ta samu tarba daga shugabannin gidan gyaran halin, sun kuma yaba ma ƙoƙarin Gidauniyar akan wannan aikin alheri, wanda Allah ne kaɗai zai biyasu. 

Inda sukayi kira ga sauran Al'umma masu hannu da shuni da su taimaka domin akwai irin waɗannan mutanen da dama da matsalar bashi ta kawo su nan gidan gyaran hali.

RMC HAUSA 

Post a Comment

Previous Post Next Post