Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Katsina ta karɓi sabbin Mataimakan Sufetandan ‘Yan Sanda (ASPs) guda 29 da aka turo daga Kwalejin ‘Yan Sanda ta Najeriya da ke Wudil.
Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar, CP Bello Shehu, ya taya su murna tare da jaddada bukatar su yi aiki da kwarewa, ladabi, gaskiya da kuma mutunta haƙƙin bil’adama yayin gudanar da ayyukansu.
An raba sabbin ASPs ɗin zuwa wuraren aikinsu daban-daban domin su taimaka wajen ƙara tabbatar da zaman lafiya da tsaro a faɗin Jihar Katsina.
RMC HAUSA
Category
labarai