Gwamna Dikko Raɗɗa Ya Buɗe Ɗakin Kwanan Ɗalibai Maza Na Jami’ar Alqalam, Ya Ƙaddamar Da Sabbin Ayyukan Cigaba
Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa, PhD, CON, ya buɗe ɗakin kwanan ɗalibai maza na farko na Jami’ar Alqalam da aka sanya wa suna “Dikko Raɗɗa Hall”, a wani biki na musamman da ya gudana a harabar jami’ar da ke Katsina.
Buɗe ɗakin kwanan, wanda aka gina domin inganta walwalar ɗalibai da ƙarfafa cigaban ilimi, ya gudana ne ƙarƙashin jagorancin Shugaban Jami’ar Alqalam, Farfesa Nasir Musa Yawuri, tare da halartar manyan jami’an gwamnati, shugabannin jami’a, da baƙi na musamman.
A yayin taron, Gwamna Raɗɗa ya kuma ƙaddamar da wasu muhimman ayyukan more rayuwa a jami’ar, ciki har da:
• Buɗe sabon titi a cikin jami’ar mai suna Sani Zangon Daura Road
• Miƙa motoci ga ma’aikatan jami’ar
• Miƙa bas ta musamman domin sufuri na ɗalibai
• Ƙaddamar da sabon ɗakin karatu domin inganta harkokin koyarwa da bincike
Da yake jawabi a wajen taron, Gwamna Dikko Raɗɗa ya bayyana cewa gwamnatin sa ta ɗauki ilimi a matsayin ginshiƙin cigaban al’umma, yana mai jaddada cewa saka hannun jari a ilimi na nufin saka hannun jari a makomar jihar Katsina.
“Wannan ɗakin kwanan da sauran ayyukan da muka ƙaddamar yau na daga cikin ƙudurin gwamnatin mu na tallafa wa cibiyoyin ilimi domin su samar da ingantaccen muhalli ga ɗalibai,” in ji gwamnan.
Gwamnan ya samu rakiyar Mataimakin Gwamna, Hon. Faruk Lawal Joɓe; Ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar Musawa/Matazu, Hon. Abdullahi Aliyu; da Ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar Jibia/Kaita, Hon. Sada Soli Jibia.
Sauran manyan baƙin da suka halarci taron sun haɗa da Daraktan Kuɗi da Mulki na Hukumar Raya Tafkin Sokoto–Rima, Alhaji Ibrahim Abubakar (Marketer), da ɗaya daga cikin shugabannin gudanarwa na jami’ar, Alhaji Biliya Sanda, tare da sauran jami’an gwamnati da al’umma.
RMC HAUSA
Category
labarai