RMC Hausa
LIVE Radio

RAMIN ƘARYA...

Kotu a Kano ta aike da mutane biyu da ake zargi da bayar da labarin ƙarya dangane da kisan Dorayi Chiranci zuwa gidan yari, har zuwa ranar 4 ga Fabrairu, 2026, domin ci gaba da shari’a.

Mai magana da yawun rundunar ƴansandan jihar Kano, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar da gurfanar da mutanen a gaban kotu, kamar yadda ya bayyana a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook ranar Juma’a.

Idan za a iya tunawa dai, bidiyon mutanen biyu ya karade shafukan sada zumunta inda ake zargin sun bada bayanin shaidar zur kan kisan uwa da 'yayanta 6 a unguwar Dorayi Chiranchi da kuma kama waɗanda ake zargi da kisan.

RMC HAUSA 

Post a Comment

Previous Post Next Post