Kwanturolan Kwastam na Katsina Ya Kai Ziyarar Aiki Ga Jami’ansa a Kan Hanyar Jibia Da Shugaban Karamar Hukumar Jibia
Kwanturolan Kwastam na Katsina, Comptroller Mohd. Saidu Musa, ya jagoranci rangadin duba aiki a kan hanyar Jibia zuwa iyakar Nijeriya da Jamhuriyar Nijar.
Wannan dai na ƙunshe ne a cikin sanarwar da Bello Isah, Jami’in Hulɗa da Jama’a na hukumar Kwastam din a jihar Katsina ya fitar a madadin Kwanturolan Yankin a ranar 10 ga watan Janairu, 2025.
Rangadin, wanda aka gudanar a ranar Juma’a, 9 ga Janairu, 2026, ya gudana ne karkashin wakilcin Mataimakin Kwanturola mai riƙon kula da sashen tsaro, Assistant Comptroller Umar Abubakar Kigo.
A yayin ziyarar, sun duba matakin ladabi, ƙwarewa, bin doka da kuma shirin aiki na jami’an da ke bakin aiki.
Ya yaba wa jami’an bisa jajircewa, ƙwazo da sa ido wajen sauke nauyin da aka ɗora musu, tare da jaddada musu muhimmancin kasancewa masu bin doka da nuna ƙwararranci a dukkan ayyukansu.
Bayan kammala rangadin duba aiki, shugabannin Kwastam sun kai ziyarar aiki ga Shugaban Karamar Hukumar Jibia, Alhaji Surajo Ado, domin ƙarfafa haɗin kai da kyakkyawar alaƙa tsakanin Hukumar Kwastam da hukumomin ƙananan hukumomi a yankin.
Da yake jawabi yayin ziyarar, Shugaban Karamar Hukumar Jibia ya bayyana godiya bisa ziyarar, tare da yabawa Kwastam na Katsina bisa jajircewa wajen tabbatar da zaman lafiya, tsaro da daidaiton harkokin kasuwanci a yankin iyaka.
Ya ce ayyukan jami’an Kwastam sun taimaka matuƙa wajen rage safarar haramtattun kaya da ƙara tsaro ga al’umma, tare da tabbatar da ci gaba da ba da cikakken goyon baya daga ɓangaren Karamar Hukumar.
A nasa martanin, Kwanturolan Kwastam na Katsina ya gode wa Shugaban Karamar Hukumar bisa goyon baya da haɗin kai, yana mai jaddada cewa kyakkyawar fahimta da haɗin gwiwa tsakanin Kwastam, hukumomin ƙananan hukumomi da al’umma na da matuƙar muhimmanci wajen cimma manufofin Hukumar.
Ya kuma sake tabbatar da kudirin Kwastam na Katsina na ci gaba da aiki tare da dukkan masu ruwa da tsaki domin ƙarfafa tsaro, bunƙasa tattalin arziƙi da cigaban al’umma a yankin.
RMC HAUSA