RMC Hausa
LIVE Radio

DIKKO RADDA

Daga yanzu kowane wata zamu lissafa haƙƙin Ma'aikatan da suka aje aiki ko suka rasu tare da biyansu kuɗaɗensu - Gwamna Radda 

Gwamnan Jihar Katsina Malam Dikko Umaru Raɗɗa ya ƙaddamar da biliyan 21 domin biyan kuɗaɗen Garatuti ga Ma'aikatan Kananan hukumomi da na jiha da Ma'aikatan da ke aiki a hukumomin ilimi da suka ajiye aiki daga Shekarar 2019 zuwa watan Oktoba na Shekarar 2025.

Gwamnan ya ƙaddamar da biyan kuɗaɗen ne a Filin Wasa na Muhammad Dikko dake cikin garin Katsina, inda ya samu halartar manyan jami'an gwamnati da tsaffin Ma'aikatan da suka ajiye aiki.

A cewar Malam Dikko Umaru Raɗɗa wannan biyan kuɗaɗen shine kashi na ƙarshe ga dukkanin Ma'aikatan da suka ajiye aiki kuma suke bin gwamnatin jihar Katsina kuɗaɗen haƙƙin su.

Gwamnan yace daga Shekarar 2023 zuwa yanzu, Gwamnatin Jihar Katsina ƙarƙashin jagorancin sa ta amince da sakin Naira biliyan 45 domin biyan haƙƙoƙin Ma'aikatan da suka ajiye aiki a jihar Katsina.

Gwamnan yace tuni Gwamnatin ta kafa hukumar kula da fansho wata Katsina State Pension Transition Board da kuma Katsina State Pension Bureau, wanda dukkanin su za su taimaka wajen kula da biyan haƙƙoƙin Ma'aikata.

Gwamnan ya ƙara da cewa, dukkanin wani tsari da Gwamnatin Jihar Katsina take fitowa da shi, to tayi shine domin ci gaban al'ummar jihar Katsina.

Malam Dikko Umaru Raɗɗa, yace biyan hakkokin na daga cikin alƙawurran da Gwamnatin sa ta dauka, inda gashi nan ta biya haƙƙoƙin.

Yace ko a farkon Gwamnatin sa, Ya amince da biyan tsaffin Ma'aikatan garatuti da suka ajiye aiki daga Shekarar 2019 zuwa shekarar 2023.

Shugaban Ma'aikatan Jihar Katsina Alhaji Falalu Bawale yace , Gwamnatin Jihar Katsina daga wannan biyan Naira biliyan 21, to ta kammala biyan dukkanin haƙƙoƙin Ma'aikatan da suke bin jihar kuma suka ajiye aiki.

A nashi jawabin, Shugaban Hukumar kula da Fansho na jihar Katsina Alhaji Mukhtar Ammani Aliyu, ya bayyana cewa Gwamnan ya amince da shirya taron ne bayan Ƙungiyoyin Ƙwadago sun buƙaci hakan.

A nasu jawaban daban-daban, Shugaban Kungiyar Ƙwadago ta NLC Comrade Hussaini Hamisu Yanduna da na TUC Comrade Muntari Abdu Ruma da Mataimakin Shugaban ƴan Fansho na Ƙasa, sun jinjinawa Gwamnan kan yadda ya sanya murmushi a fuskokin tsaffin Ma'aikatan, ta hanyar biyan su haƙƙoƙin su.

RMC HAUSA 

Post a Comment

Previous Post Next Post