Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Ambasada Ismail Abba Yusuf a matsayin sabon shugaban hukumar Alhazai ta kasar, NAHCON, kamar yadda mai taimaka masa na musamman kan yada labarai Bayo Adenuga ya faɗa a wata sanarwa a ranar Laraba.
Naɗin nasa na zuwa ne bayan da Farfesa Abdullahi Usman Saleh ya yi murabus daga mukamin a farkon makon nan.
Sanarwar Fadar Shugaban Kasar ta ce Tinubu ya aika wasiƙa ga shugaban majalisar dattijai Godswill Akpabio, yana mei neman a yi gaggawar tabbatar da nadin sabon shugaban NAHCON din.
Ambasada Yusuf ƙwararren jami’in diflomasiyya ne.
RMC HAUSA
Category
Labarai