Majalisar zartarwa ta jihar Katsina ta amince da wasu tsare-tsare da ayyuka da nufin ƙarfafa ɓangaren ilimi, haɓaka shugabanci na zamani, inganta tsare-tsaren birane, da kuma haɓaka ayyukan sauyin yanayi a faɗin jihar.
An amince da waɗannan shawarwarin ne a lokacin taron majalisar zartarwa ta jiha karo na 5 na shekarar 2026, wanda aka gudanar ranar Alhamis a zauren majalisar zartarwa ta Janar Muhammadu Buhari, GMB, House, a Katsina.