*WATA SHAWARA*
Da sunan Allah Mai Rahama Mai jinƙai.
Fatan an sha ruwa lafiya. Ko ba komi kila wani ya ce na cika tsogumi ko hayyata dangane da al'amarin da ya shafi masana'antar shirya Fim musamman a Jihar da nake wato Katsina. Kamar kowane lokaci Yau ma dai hakuri kawai zan iya Baku Amman sai na Kara Bada wata shawarar ko Allah Ya sa shuwaganninmu da dattawan da ke cikin harkar tare da masu kishi da Hali a cikinmu za su dauki mataki na gyara.
Duk da kasancewata shekaru 25 Ina gudanar da wannan harkar Amman har yanzu idanuwana na ganin akwai wurare masu Tarin yawa da aka wuce mu Ina nufin mu katsinawa.
Misali:-Bangaren Samar da ingantaccen labarin Fim, Bangaren kyankyashe jarumai Maza da mata, Bangaren Bada Umarni, Bangaren tace Fim (Editing) da sauran wasu bangarori.
A ganina sai na ke hasashen cewa Shuwagabannin Kungiyoyin MOPPAN, AREWA FILM MAKERS, KATSINA FILM INDUSTRY, GWAGWARE FILM MAKERS. Da sauran manyan masu kamfanonin shirya fina-finai na Jihar Katsina Misali:-Lawan Ahmad Mai Kamfanin BAKORI ENTERTAINMENT, LAWAL. BAWON MATA, BALARABE SUPER STAR, Da sauran wadanda ya kamata su Rika shirya mana tarukan karawa juna sani, ta yadda za a Rika gayyato wani masani a bangarori misali yadda ake Samar da ingantaccen labari, Ko yadda ake Bada Umarni ya Rika yi mana darasi akan Hakan.
Ina ganin sannu a hankali za mu Kara samun ilimin yadda ake gudanar da wannan sana'a ta film.
Amman dai wannan shawara Ce.
Daga:-
SHAMSUDDEEN IBRAHIM FATIMIYYAH
(Tsohon shugaban Kungiyar Marubutan Jihar Katsina KMK)
RMC PLUS
Category
Nishaɗi