Jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC) ta ware tikitin takarar shugaban ƙasa na shekarar 2027 ga yankin Kudancin Nijeriya.
Jam’iyyar ta cim ma wannan matsaya ne a yayin babban taronta na ƙasa da aka gudanar a Abuja ranar Asabar.
NDC ta bayyana cewa tikitin shugaban ƙasar zai kasance na wa’adin mulki guda ɗaya na shekaru huɗu kacal. Ta kuma ware tikitin takarar shugaban ƙasa na shekarar 2031 ga yankin Arewacin Nijeriya.
Wannan na zuwa ne yayin da shugabannin jam’iyyar ciki har da Peter Obi, Rabiu Kwankwaso da sauran manyan jiga-jigai ke taro a Abuja domin gudanar da babban taron ƙasa na jam’iyyar.
Ana sa ran taron zai tabbatar da wasu daga cikin matakan da kwamitin zartarwa na ƙasa na NDC ya ɗauka a baya-bayan nan.
Bisa ga ajandar da aka bai wa ‘yan jarida, batutuwan da za a tattauna sun haɗa da tsarin rabon muƙamai, amincewa da kundin tsarin mulkin jam’iyyar da aka yi wa gyara, da kuma zaɓen shugabannin jam’iyyar na ƙasa.