RMC Hausa
LIVE Radio

TARON RENEWED HOPE HOUSING A ABUJA

Ministan Gidaje Da Sauran Manyan Baƙi Sun Halarci Taron Renewed Hope Housing PPP Summit A Abuja

Ministan Gidaje da Raya Birane na Tarayya, Muttaqha Rabe Darma, tare da wasu manyan baƙi da jami’an gwamnati, sun halarci taron “Renewed Hope Housing PPP Summit” da aka gudanar a Cibiyar Taro ta Shehu Musa Yar’Adua da ke Abuja.

Taron ya haɗa masu ruwa da tsaki a bangaren gidaje da raya birane domin tattauna hanyoyin inganta zuba jari da haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu wajen samar da gidaje a ƙasar nan.

Ana gudanar da taron ne a wani ɓangare na ƙoƙarin gwamnatin tarayya na ƙarfafa manufofin samar da gidaje masu araha da bunƙasa cigaban birane a faɗin Najeriya.

Source: Mobile Media Crew

Post a Comment

Previous Post Next Post