Daga karshe tsohon mataimakin Kakakin majalisar dokoki ta Jihar Katsina, kuma tsohon Ɗan majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar Faskari, har sau uku daga shekara ta 2011 zuwa shekara ta 2023, karkashin jam'iyyar Apc.
Yanzu haka kuma shine Ɗan majalisar tarayya mai wakiltar Kankara, Sabuwa da Faskari Rt. Hon. Shehu Dalhatu Tafoki, ya fice daga Jam'iyyar Apc ya koma Jam'iyyar PDP.
Jagoran Jam'iyyar PDP ne na Jihar Katsina Sanata Yakubu Lado Ɗan Marke tare da shugaban Jam'iyyar PDP na Jihar Katsina Malam Nura Amadi Kurfi suka miƙa masa fom na takara kai tsaye ta Ɗan majalisar tarayya mai wakiltar Kankara, Sabuwa da Faskari.
Fita daga Jam'iyyar Apc da Rt. Hon. Shehu Dalhatu Tafoki ya yi bai rasa nasaba da abinda ya faru a sasancin fitar da yan takaar jam'iyyar APC a jihar katsina.